Hari Kan Jirgin Ruwan Iran Ya Lashe Ran Mutum Guda Da Jikkata Hudu

Wani mutum daya ya mutu kuma ma’aikacin jirgin ruwa ne sannan wasu ‘yan kasuwa hudu sun ji rauni bayan da wani makami ya bugi jirginsu

Wani mutum daya ya mutu kuma ma’aikacin jirgin ruwa ne sannan wasu ‘yan kasuwa hudu sun ji rauni bayan da wani makami ya bugi jirginsu a mashigar ruwan Hormuz

Hossein Amir Teymouri ya ruwaito cewa: Wani jirgin ruwa na Iran ya fuskanci bugu daga wani makami mai linzami da ba a san asalinsa ba, kusa da Tsibirin Hengam a Mashigar Hormuz a safiyar Lahadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ma’aikacin jirgin guda daya tare da jikkata wasu hudu.

Kamfanin dillancin labaran “IRNA” na kasar Iran ya ruwaito daga Amir Teymouri yana cewa: Jirgin Ruwan yana tafiya a Mashigar Hormuz kusa da Tsibirin Hengam a lokacin da lamarin ya faru, kuma yana da ma’aikatan jirgin goma a cikinsa.

A cewar rahoton, wani ma’aikacin jirgin, Jamshid Rajabi, ya mutu, yayin da wasu hudu suka jikkata lokacin da makamin ya bugi jirgin ruwan.

Gwamnan lardin Qeshm ya tabbatar da cewa: Ana gudanar da bincike don gano yanayin lamarin, yana mai lura cewa har yanzu ba a san ko daga ina aka harbo makamin ba, kuma ba a fitar da wani karin bayani game da lamarin ba tukuna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted