Da marecen jiya Litinin an ji karar bude wuta a kusa da fadar shugaban kasar a birnin Caracas,kamar yadda kamfanin dillancin labarun faransa ya nakalto.
Sai dai majiyar gwamnatin kasar ta ce daga baya bude wutar ya tsaya, ya kuma faru ne bayan da wani jirgin sama maras matuki ya yi shawagi a kusa da fadar shugaban kasa.
Wani mazaunin yankin da lamarin ya fada wa kamfanin dillancin Labarun Faransa cewa, da misalin karfe;8;00 na marecen jiya Litinin ne aka ji kararraki da yawa wanda ya yi kama da fashewar wasu abubuwa, kuma sun faru ne kusa da kusa, sai dai ba ku kai karfin na ranar Asabar ba.
Wasu hotunan bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda harbi yake tashi daga kasa zuwa sama, da haka yake nuni da cewa ana kai wa jirgin maras matuki bara ne.
Haka nan kuma an ga ma’aikatan cewa masu yawa da su ka zagaye fadar shugaban kasar.