Sojojin Kasar Labanon Sun yi Watsi Da Hadin Guiwa Kai Tsaye Da Sojojin Isra’ila

rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar labanon sun yi watsi da duk wani matakin hadin guiwa kai tsaye da sojojin HKI kan tsarin gwaji

rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar labanon sun yi watsi da duk wani matakin hadin guiwa kai tsaye da sojojin HKI kan tsarin gwaji wanda suke ganinsa a matsayin wani mataki ne da zai tsawaita zama sojojin isra’ila a kudancin labanon.

wani babban jami’a a kasar labanon ya  bayyanawa tashar talabijin din almayadeen a wata hira da ta yi da shi cewa” dakarun sojin kasar ba za su shiga cikin duk wani shirin gwaji ba,  har sai dukkan sojojin isra’ila sun fice baki daya daga yankin ,ya jaddada cewa dakarun sojin kasar sun yi watsi da duk wani shiri hadin guiwa kai tsaye da sojojin isra’ila.

haka zalika ya kara da cewa sojojin kasar ba za su yi aiki ko kadan karkashin duk wani umurni da ya hada da Isra’ila ba, aikinsu ba shi ne su share hanya ga makiya ba  inda za su samu damar shiga wasu yankunan da suka kasa shiga  saboda yan gwagwarmaya,

A baya bayan nan kwamandan dakarun sojin kasar labanon ya shaidawa shugaban kasar Joseph Aun cewa sojojin kasar sun yi watsi da duk wani shiri da ake son aiwatarwa karkashin jarjejeniyar da aka cimma tsakanin labanon da isra’ila da kasar Amurka ta shiga tsakani

Ana ta bangare kungiyar hizbullah ta kasar labanon tuni tayi watsi da shirin kuma tana ganinsa a matsayin wani yunkuri ne na neman sasssaucin ra’ayin yan siyasa da kuma kare kasancewa sojojin da da hare haren da take kai musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted