Wani babban kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran ya bayyana cewa dole ne Iran ta kai matsayinda zata kai farmaki cikin kasashe makiyan nisa da kan iyakokin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar iran ya nakalto Burgedia Janar Mohammad Reza Naghdi yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa a halin yanzun yawan makamai masu linzami samfurin balistic da ake amfani da du sun dara abinda ake iya cillawa a ko wace rana, ya kara da cewa Iran zata dau shekaru tana cilla makaman bilistic na makiya na shekaru, haka ma jiragen Drones masu kunan bakin wake, samar da su ya fi yawan wadanda ake cillawa a ko wace rana a lokacin yaki.
Janar Naghdi y ace, a halin yanzu dakarun sun sami umurnin kare makamai masu linzami wadanda suke kaiwa nesa da kan iyakokin kasar Iran, kuma za’a samar da su kafin su sami umurnin amfani da su. Daga karshe yace, sojojin Iran sun hada Amurka kaiwa ga manufofinsu guda 14 da suka shiga yaki da Iran da su.