Iran Tana Juyayin Wafatin Manzon All..(s) Da Jikansa Al-Hassan(a)

Mutanen Iran a yau Laraba 28 ga watan Safar na wannan shekarar suna cikin juyayin shadar manzon All..(s) wanda ya  kasance rahama ga talikai, kuma

Mutanen Iran a yau Laraba 28 ga watan Safar na wannan shekarar suna cikin juyayin shadar manzon All..(s) wanda ya  kasance rahama ga talikai, kuma wanda ya budewa bil’adama hanyar nasara a rayuwa ta duniya da Larahira har duniya ta nade.

Har’ila yau suna juyayin shahadar jikinsa babba kuma wasiyinsa na biyu Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) wanda shi ma yayi shahada a ranar irin ta yau a hannun mafi sharri daga cikin sarakunan banu umayya a lokacin.

Muna taya al-ummar musulmi juyajin wadan nan shahidai wadanda ba zamu iya kwatanta girman rashin nasu da duk wani irin rashi ba. Ranar shahadar manzon All..(s) rana she wace dukkan masoya iyalan gidan manzon All..(s) suke cikin bakin ciki har yau, saboda rashinsa (s) mafari ce ta manya manyan musibun da suka fadawa musulmi a bayansa.

Haka ma ranar shahadar Imam Al-Hassan (a) rana ce ta bakin ciki ga dukkan wadanda suke kaunar iyalan gidan manzon All..(s), sabod shi ne fitila ta gaskiya ta farko bayan kakansa da da mahaifinsa. Shi ne tauraro na biyu wannan al-ummar musulmi ta rasa bayan kakansa(s).

Da fatan All..ya arzutamu da cetonsu a ranar da babu mai cewa sai ga wanda All..yayi wa izinin ceto.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted