Himmati: Iran Zata Shiga Bankin BRICS Nan Ba Da Dadewa Ba

Iran zata zama mamba a cikin bankin kungiyar raya tattalin arziki ta BRICS, wato New Development Bank (NBD), wanda ya kasance bangare mai muhimmanci da

Iran zata zama mamba a cikin bankin kungiyar raya tattalin arziki ta BRICS, wato New Development Bank (NBD), wanda ya kasance bangare mai muhimmanci da kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto gwamnan babban bankin JMI Abdunnasir Himmati yana fadar haka , ya kuma kara da cewa, Iran tana fatan zata fadada huldar kudade da mambobin wadan kungiyar wanda zai fadada harkokin kasuwanci musamman na kudade da manya manyan kasashen wannan kungiyar.

Himmati ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda yake halattan tarin kungiyar ta BRICS a kasar India, ya kuma kara da cewa sabon bankin raya kasashe kungiyar NDB shi ne cibiya mafi muhimmanci a kungiyar BRICS kuma Iran zata kasance mamba a cikin bankin nan gaba kadan.

Gwamnan ya kuma yabawa kasar India a lokacinda ta rike shugabancin kungiyar a cikin yan shekarun da suka gabata, sannan ya kara da cewa a cikin wannan lokacin ayyukan musayar kudade tsakanin mambobin kungiyar ya karu haka ma, tattalin arziki na kumfuta ya kara karfi a tsakaninsu.

Daga karshen ya ce, a cikin kungiyar BRICS ne kasar Iran take haduwa da kasashe wadanda ta fi hulda da su a fagen tattalin arziki da kudade. Don haka dam ace babba ga kasar Iran.

Himmati ya je kasar India ta tawaga mai yawa na jami’an gwamnati da yan kasuwa na kasar Iran inda ya halarci, taron gwamnonin kasashe masu alaka da bankin BRICS.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted