Kasar Chadi na gudanar da gagarumin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai a daidai da 11 ga watan Agusta, wanda tuni shugabannin kasashen Afirka daban-daban suka isa babban birnin kasar, N’Djamena, domin taya al’ummar kasar murna da kuma nuna goyon baya na diflomasiyya.
Wannan biki, yana da mahimmanci na tarihi tunda kasar ta tsallake daga hannun mulkin mallaka na kasar Faransa a ranar 11 ga Agustan 1960, lamarin da ya kawo karshen shekaru masu yawa na danniya da babakere.
Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ne ke jagorantar wannan babban biki, inda tsare-tsaren suka hada da faretin dakarun soji na musamman da nuna fasahar tsaro, hadi da jawabai na nuna kishin kasa da manufofin bunkasa tsaro da zaman lafiya.
Babban abin da ya dauki hankali a wannan lokacin shi ne, sanarwar da shugaban kasar ya fitar na janye bizar shiga Chadi ga dukkanin ‘yan Afirka, wanda hakan babban mataki ne na dunkulewar nahiyar.
Wannan sabon tsari na tafiya ba tare da biza ba zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2027, da nufin saukaka zirga-zirgar mutane, bunkasa harkar yawon buɗe ido, da kuma janyo hankalin masu zuba jari a cikin Afirka.