Dakarun sojin HKI na ci gaba da cin karansu ba babbaka a kudancin labanon wajen kai hare hare da rusa gidajen mutane inda suka nufi wasu garuruwa da yankuna a lokaci guda kuma suna rushe filaye da gidaje,
Da sanya safiyar yau laraba ma sojojin isra’ila sun harba wasu abubuwan fashewa a garin qantara da kuma manyan makamansu sun kai hari a kan tsaunukan Ali al-tahir kamar yadda gidan talabijin din Al mayaden ya bayyana, kuma bayan haka jiragen yakin Isra’ila sun kai hari a gefen garin hajeer kuma suka harba abubuwa masu fashewa a garin hadatha
Majiyar labaran gwamnatin ta sanar da shahadar mutum guda da safiya yau a garin nabadiya a Asbitin najdatu shaabiya sakamakon mummuna rauni da yaji bayan harin da isra’ila ta kai a kan motarsa a kan hanyarsa ta zuwa garin kufrruman a ranar talata.
haka zalika ya kara da cewa dakarun sojojin Isra’ila sun yi amfani da wasu naurori wajen lalata filaye da gidajen mutane da hanyoyi a garin rub salasin, da kuma kona gidaje a garin Khayyam da hadatha, kuma sun tarwatsa gidaje da abubuwan mure rayuwar jama’a a zudur sharkiyya da majdal zun, da bani hayyan,