Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta bada labarin cewa tawagar tattaunawar kasar ta sami sakon na musamman daga gwamnatin kasar Saudia zuwa birnin Masqat na kasar Omman don tattauna batun kawo karshen yaki a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran a birnin San’aa, ya bada sanarwan cewa, bayan hare hare masu zafin da dakarun Ansarallah na kasar Yemen suka kai kan sojojin Saudia a kudancin kasar yemen da kuma wasu da suka kai cikin kasar ta Saudia, wadanda duk suka halaka sojojin saudia da dama, gwamnatin saudia ta aikawa tawagar tattaunawa ta Ansarallah sako na musamman don kawo karshen yaki a tsakaninsu a birnin Makat na kasar Omman.
A cikin sakon gwamnatin kasar Saudia ta bukaci tawagar Ansarallah ta shiryawa kawo karshen yaki a kan yarjeniyar da suka cimma tsakaninsu a shekara ta 2022 a wanda ake kira Riyad –san’aa.
Labarin ya kara da cewa, jami’an gwamnatin Ansarallah sun ki amince da wannan sakon gaba daya, inda suka kara da cewa kawo karshen yakin ba shi ne kadai bukatar gwamnatin Yemen ba, sun kuma kara da cewa dole ne saudia da farko ta kawo karshen killacewar da takewa kasar ta biya diyya ta kuma kawo karshen shishigi a cikin al-amuran kasar Yemen kwata kwata. Wanda yarjeniyar 2022 bai ambacesu ba.