Babban jam’in tsaro na kasar iran ya bayyana cewa za’a bude mashigar Hurmuz a tekun fasha ne inda iran ta sanya tsauraran matakai kan jirgen ruwa dake zirga-zirga a wajen tun a farkon watan maris saboda hare-haren da Amurka da isra’ila ke kai wa iran , kuma zaa bude ta ne kawai duk lokacin da Amurka ta amince da sharuddan da iran ta shinfida
Muhsin Riza’I sabon shugaban majalisar koli ta tsaron kasa da aka nada a baya bayan nan ya shaidawa jakadan kasar rasha a Tehran ZONG PIYU a wata ganawa da suka yi a jiya talata cewa dole ne Amurka ta kawo karshen yaki da take yi da iran da ma sauran kawayenta a yankin, kuma ta saki dukkan kadarorinta da take rike da su,kafin a bude mashigar Hurmuz
Yace matukar kasar Amurka ba ta canza halayenta ta ba, kuma bata amince da sharuddan iran ba to mashigar Hurmuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe ba zaa iya bude ta ba. kuma ya jaddada cewa iran da oman da sauran kasashen dake da baki a mashigar Hurmuz suka cimma matsaya game da batun yin zango a hanyoyin ruwa to wannan ba zai yi tasiri game da matakin da iran ta dauka na rufewa ko bude mashigar Hurmuz ba
Ana sa bangaren jakadan kasar china a iran Zong piyo ya jaddada matsayin china na nuna adawa da hare haren da Amurka da isra’ila ke kaiwa kasar iran, yace shugaban china xi jinping ya sanya wasu tsare-tsare guda 4 na samar da zaman lafiya da tsaro a yammacin Asiya