Sojojin Isra’ila Sun Kai Hari A Kan Masallatan Nablus A Ranar Juma’ar Farko Ta Watan Ramadan

Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan.

Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, a safiyar ranar Juma’a sojojin gwamnatin Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu masallatai shida na birnin Nablus, inda suka hana gudanar da salla.

Har ila yau, sun kame wasu Falasdinawa uku a lokacin da suke kutsawa cikin Nablus.

Rahotanni sun ce sojojin na Isra’ila sun harba harsasai masu rai, da gurneti da bama-bamai masu guba a yayin da dakarunsu suka mamaye wasu unguwanni a birnin.

Ko a ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ci gaba da cin zarafi da gwamnatin Isra’ila ke yi kan yankin yammacin kogin Jordan na daga cikin shirin gwamnatin kasar na mamaye yankin.

A watan Yulin 2024, Kotun Duniya (ICJ) ta yanke hukuncin mamayar da Isra’ila ta dade tana yi a yankunan Falasdinawa ba bisa ka’ida ba, inda ta bukaci a kwashe duk wasu haramtattun matsugunan da ke Yammacin Kogin Jordan da gabashin Quds.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments