A yau ce falasdinawa a Gaza suka gudanar da jana’izar mutane 100 wadanda aka zakulo gawakinsu daga burbushin gine gine a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto majiyar kungiyoyin fararen hula a Gaza na cewa sun zakulo gawakin Falasdinawan ne bayan kwanaki na aikin kwace burbushin gine gine a yankin.
Labarin ya kara da cewa an gudanar da jana’izar ne a unguwar Zaitun na gabacin birnin Gaza. Kuma ana zaton wasu gawaki kima 8000 suna bisne a karkashin taron buraguzan gine gine a gazar.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza, ya kara da cewa tun ranar 11 ga watan Octoban shekara ta 2024, yahudawan sun kashe falasdinawa 1,344 sannan wasu 4,464 suka ji rauni. Wannan kuma ya daga yawan shahidai falasdinawa tun 7 ga watan Octoba zuwa 73,651 sannan yawan wadanda suka ji rauni kuma zuwa 174,575.