Iran: Muna Bukatar Rabo Babba A Kasuwar Jan Karfe A China

Yan kasuwar kasar Iran masu hakar ma’adininin jan karfe, ko Copper sun bayyana anniyarsu ta shiga kasuwar jan karfe na kasar china wacce take kara

Yan kasuwar kasar Iran masu hakar ma’adininin jan karfe, ko Copper sun bayyana anniyarsu ta shiga kasuwar jan karfe na kasar china wacce take kara fadi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Masuod Ostad –Hussain Jami’i a cibiyar kasuwanci na kasar Iran yana fadar haka, ya kuma kara da cewa a a shekara ta 2024 Iran ta sayar da jan karfe na kimani dalar Amurka miliyon $618 a kasuwannin duniya, wanda ya bada matsayi na 50 a duniya.

Ya kara da cewa, kasar Turkiya ce take gaba a sayan jan karfe daga Iran, wanda ya kai dalar Amurka miliyon $474, sai kasar China wacce take binta da dalar Amurka miliyon $126.

Don haka kasar China ce kasar ta farko a wajen yammacin Asia wacce take sayan jan karfe na Iran, wanda kuma yakamata a fadadata. Cibiyar kasuwanci ta Iran ta bayyana haka a yau Lahadi, ta kuma kara da cewa yakamat ta fadada yawan jan karfen da ke zuwa kasar China daga Iran don cimma wannan manufar.

Cibiyar ta kara da cewa farashin jan karfe a kasuwar china ya karu daga dalar Amurka $2,305 kan ko wani ton a shekara ta 2025, zuwa dalar Amurka $2,909 kan ko wani ton a shekara ta 2026 da muke ciki.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted