Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mutane 4 sun yi shahada yayin da wasu 20 su ka jikkata sanadiyyar hare-haren sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Harin na safiyar Lahadi dai an kai shi ne kudancin kasar, ya kuma shafi kananan yara 3 kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiyar ta sanar.
A garin Arabsalim dake kudancin kasar ta Lebanon mutane biyu ne su ka yi shahada, kamar kuma yadda ‘yan sahayoniyar su ka kai hari a wani gida ta hanyar amfani da jirgin saman a yaki.
A garin Kafar-Ruman kuwa wasu mutane 5 ne su ka jikkata bayan da ‘yan sahayoniyar su ka yi amfani da manyan bindigogi wajen kai hari akan wani gida.
A gefen garin Nabadhiyyah kuwa, sojojin mamayar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki wajen kai hari, sannan kuma su ka kai wani harin da jiragen yaki a cikin garin. Mutane da dama ne dai su ka jikkata sanadiyyar hare-haren biyu.
Kafafen watsa labarun kasar ta Lebanon sun ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun rusa asibitin garin “Gandur’ tare da baje shi da kasa.
Haramtacciyar Kasar Isra’ila ba ta girmama yarjejeniyar tsagaita wutar da ta cimmawa da gwamnatin kasar Lebanon, inda take ci gaba da kai hare-hare akan yankunan kasar mabanbanta,musamman a kudancin kasar.