Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya gargadi makiya, musamman Amurka kan cewa, daga yanzun kuma maida martani ba zai kasance ido da ido kunne da kunne ba, sai dai kamar yadda ya faru a hare haren baya bayan non zamu rika maida martani ne gwagwadon gannin damarmu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin majalisar dokokin kasar Iran na fadar haka a safiyar yau Lahadi a zaman majalisar dokokin kasar ta Iran.
Ya kuma kara da cewa maida martani na baya bayan nan mataki na farko ne, A hare hare na baya bayan nan Iran ta yi amfani da fannonin yaki daban daban, daga cii da fasahar AI don samar da hotunan bidiyo a fagen fama.
A yanzun kuma da makiya suka fara yakin tattalin arziki nag aba daya a kan kasar Iran zamu bullo da wasu hanyoyi da zasu taimakawa wannan nau’in yaki, ga masu hulda da kasar da kuma hanyoyin kaucewa duk wata cuta.