Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu.

Shugaban kasar iran Msud pezeshkiyan ya kira prime ministan Iraqi mohammad shia al-sudani ta wayar tarho domin taya shi murnar kammala zaben yan majalisar dokoki

Shugaban kasar iran Msud pezeshkiyan ya kira prime ministan Iraqi mohammad shia al-sudani ta wayar tarho domin taya shi murnar kammala zaben yan majalisar dokoki da aka yi a kasar cikin gagarumar nasara da kuma kwanciyar hankali da tsaro.

 Kasashen iran da Iraqi kasashe ne masu makwabtaka da juna kuma sakamakon  da aka fitar na zaben yan majalisa da aka gudanar zai taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu,

Ana sa bangaren Al-sudani ya jaddada cewa zaben ya nuna irin yadda alummar iraki suka yi riko da demukuradiya, kuma sakamakon zaben zai taimakawa kasar wajen gudanar da ayyukan ci gaba  da gina kasar da gwamnatin tasa a gaba,

Shi ma shugaban iran pezeshkiyan  ya jinjina game da yadda aka gudanar da zaben kuma ya bayyana shi a matsayin babbar nasara,da ya kare mutuncin mutanen iraki, kuma yayi fatan cewa dangantakar dake tsakanin za ta kara zurfi a sauran shekaru masu zuwa.

Dukkan shuwagabannin sun nuna aniyarsu ta kara fadada dangantaka dake tsakanin da kuma yin aiki tare a yankin ,kuma sudani ya yi fatan ganin an kara karfafa dangantaka a bangarorin daban-daban a tsakaninsu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted