Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta

Dakin Gwaje-gwaje na “Sandia” dake karkashin ma’aikatar makamashin Amurka ya sanar da cewa; Jirgin sama samfurin “F-35” ya jefa bom din Nukiliya ba tare da yana dauke da abubuwan da suke fashewa a ciki ba. Majiyar ta kara da cewa an yi wannan gwajin ne dai a yankin Nivada na kasar ta Amurka a tsakanin […]
Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000

Jamhuiryar Demokradiyyar Congo ta fitar da ma’adanin ‘Colbat’ da ya kai ton 1,000 a karon farko. Shi dai wannan ma’adanin ne ake amfani da shi wajen yin batirin “Lithium-ion” masu cajin motoci mai amfani da wutar lantarki, wayoyin hannu, kwamfuta da suaransu. Bugu da kari wannan ma’adanin yana taka rawa wajen kauracewa amfani da makamashin […]
Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa

Jaridar “ma’ariv’ ta buga labarin dake cewa Fira minista Netanyahu yana rayuwa cikin zullumi da tsoro mai tsanani akan hukuncin da kotu za ta yanke masa. Jaridar ta ‘yan sahayoniya ta kuma ce yadda ake yin matsin lamba daga waje domin ganin an yafe wa Netanyahu,yana nuni ne da yadda Fira ministan yake cikin tsoro […]
An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza

Kungiyar “Oil Change International” mai zaman kanta ta bayyana cewa da akwai kasashe 25 da su ne su ka rika sayar wa da “Isra’ila” man fetur a tsawon lokacin yakin Gaza. Rahoton wannan jaridar ya yi ishara da kasashe 25 da su ne madogarar Haramtacciyar Kasar Isra’ila” wajen samun makamashin da ta rika amfani da […]
MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan

Hukumar dake kula da ‘yan hijira ta MDD ta ce; Da akwai fiye da mutane 100,000 da su ka fice daga birnin Al-Fasher makwanni biyu kadai bayan da da kungiyar RSF ta shimfida ikonta a cikinsa. Mai magana da yawun hukumar ‘yan hijirar ta MDD, ta kuma ce abu ne mai yiyuwa a halin yanzu […]
Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba

Rahotanni sun bayyana cewa jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeid Iravani yayi gargadin cewa Tehran ba za ta taba mika wuya ga matsalin lmbar soji ba, ko ta siyasa ko kuma takunkumin tattalin Arziki, kuma ta yi tir da Amurka da Isra’ila game da harin da ta kai kan tashoshin nukiliyarta da ya […]
Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela

Rahotanni sun nuna cewa kasashen latin Amurka sun gudanar da tattaunawa na shirya fitar da sanarwa ta hadin guiwa na shirya mayar da martani kan duk wani hari da kasar Amurka za ta kai a kan kasar Venuzuela, Wakilan diplomasiya na kasashen daban daban sun shirya tuntubar juna domin shirya ma duk wani shirin Amurka […]
Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha mariya zakhrova ta bayyana cewa Mosko ba ta da wani shirin na kai hari kan wata mamba a kungiyar tsaro ta Nato amma ta shirya mayar da martani kan duk wanda ya kai mata hari daga mambobin kungiyar. Da take taron manenma labarai mariya ta zayyana cewa tana kara […]
Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu.

Shugaban kasar iran Msud pezeshkiyan ya kira prime ministan Iraqi mohammad shia al-sudani ta wayar tarho domin taya shi murnar kammala zaben yan majalisar dokoki da aka yi a kasar cikin gagarumar nasara da kuma kwanciyar hankali da tsaro. Kasashen iran da Iraqi kasashe ne masu makwabtaka da juna kuma sakamakon da aka fitar na […]
M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan

Babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterre yayi kakkausar suka game da harin da yahudawa yan share wuri zauna suka kai kan wani masallaci da ya kai ga konewa a Dair Istiya dake yankin da isra’ila ta mamaye a gabar yamamcin kogin jodan, Matakin na majalsiar dinkin duniya na yi tir da kai […]
Mali ta Dakatar da Tashoshin Talabijin na Faransa TF1 da LCI

Hukumomin Mali sun dakatar da watsa shirye-shiryen tashoshin gidajen talabijin na kasar Faransa TF1 da LCI a fadin kasar. Hukumar Sadarwa ta Mali ta bayar da dalilan dakatar da wadanan tashohin bisa wani shiri da tashar LCI ta yi kan halin da ake ciki sakamakon matsalolin tsaro masu nasaba da kungiyoyin dake ikirari da sunan […]
Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin Trump

Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da shirin zaman lafiya na shugaba Donald Trump. Amurkar da wasu abokan huldarta na kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya “yi sauri” ya amince da daftarin kudurin Amurka wanda ya amince da shirin zaman lafiya […]
AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro

Kungiyar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun karfafa kawancensu kan dabarun tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba don magance kalubalen duniya da na yanki yanki. “Hadin gwiwa tsakanin kungiyoyinmu bai taba kasancewa mafi karfi da muhimmanci fiye da yadda yake a yau ba,” in ji Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya […]
Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan

Iran ta bukaci kasashen duniya dasu gaggauta daukar mataki kan halin da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher don magance matsalar dake ta’azzara a arewacin Darfour. Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Ali Bahraini, ne ya bayyanan hakan a jawabinsa yayin zaman musamman na 38 kan yanayin kare hakkin dan adam a […]
EU ta nemi Isra’ila ta dauki mataki kan tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan

Tarayyar Turai ta yi kira ga Isra’ila da ta dauki mataki nan take don kawo karshen tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan. Mai magana da yawun Hukumar Kula da Harkokin Waje ta Tarayyar Turai, na mayar da martani ne kan karuwar tashin hankalin dake da nasaba da yahudawa ‘yan kama wuri zamna da ke yi […]