Shugaban Amurka Donald Trump Ya Goyi Bayan Harin Da Kasar Saudiya  Ta kai Kan Kasar Yamen

Wasu jami’an Amurka guda biyu sun bayyana cewa Donald Trump ya sanar da goyon bayansa ga yarima mai jiran gado na kasar saudiya Mohammad bin

Wasu jami’an Amurka guda biyu sun bayyana cewa Donald Trump ya sanar da goyon bayansa ga yarima mai jiran gado na kasar saudiya Mohammad bin salman game da matakin soji da ya dauka kan filin saukar jiragen sama na birnin sana’a a kasar Yamen don hana tawagar kungiyar Ansarullah da ta je kasar iran sauka .

Dakarun kasar yamen sun bayyana cewa sun kai harin mayar da martani kan babban filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Abha da makami mai linzami na ballistic da jirage marasa matuki a kudancin kasar saudiya

Kakakin sojin kasar Yamen birgedier janar Yahya Saree ya gargadi dukkan kafanonin jiragen sama dake sauka a filiyen jiragen sama na saudiya , kuma ya yi kira da su dauki wannan gargadi da muhiammanci har sai an dauke takunkumin da aka sanyawa filin saukar jiragen sama na Sanaa.

A fege guda kuma jakadan iran na dindindin a majalisar dinkin duniya yayi watsi da zargin da ake wa iran na cewa tana aikewa da makama zuwa kasar Yamen kuma ya bayyana zargin a matsayin karya da bashi da tushe balle madafa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted