Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki

Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis

Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki

Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa.

A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.”

Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga shiga siyasa da kuma cire wakilan kungiyarsa daga majalisar dokoki, domin nuna rashin amincewa da abin da ya bayyana a lokacin a matsayin “cin hanci da rashawa da kuma biyayya ga kasashen waje.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments