Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Harin Amurka ya bayyana karara kan Venezuela Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Barazanar da ake yi wa Venezuela ba ta dace da al’ummar duniya ba, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kuma za ta ci gaba da kasancewa […]
Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu

Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya jaddada muhimmancin matakin da ake dauka a yanzu na dangantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan a dukkan fannoni na hadin gwiwa. Ya bayyana ziyararsa zuwa Pakistan […]
Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza

Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka ta bukaci duba kudurin da aka gabatar na neman kafa rundunar kasa da kasa a Gaza Rahotannin daga Amurka sun bayyana cewa: Gwamnatin Amurka ta Trump tana neman amfani da rikicin Gaza wajen kwace makaman kungiyar Hamas da take amfani da ramuka wajen yakar ‘yan sahayoniyya, […]
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon

Mutum guda ya yi shahada wasu uku kuma suka jikkata a harin da Yahudawan sahayoniyya suka kai kan yankin kudancin Lebanon An kashe mutum guda, wasu uku kuma sun ji rauni a hare-haren jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suka kai kan garin Tura da ke gundumar Taya na kasar Lebanon, a cewar wata […]
Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki

Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi […]
Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi

Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba […]
Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa Moscow za ta dauki “matakan mayar da martani” idan Amurka ta koma gwada makaman nukiliya, a yayin da ake kara samun takun saka tsakanin manyan kasashen biyu masu makamman nukiliya. A yayin wani taro da ya yi da Majalisar Tsaron Rasha a ranar Laraba, Putin ya umarci […]
Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Gwamnonin IAEA

Kasahen Iran, Rasha da kuma China sun gana a tsakaninsu a jajibirin taron Kwamitin Gwamnonin Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Zaman ya hada jakadun kasashen uku a birini Vienna ranar Laraba don daidaita matsayinsu kan manyan batutuwan da suka shafi zaman na gwamnonin IAEA da ke tafe. Michael Ulyanov, jakadan Rasha kuma […]
Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bukaci Amurka da Turai su nuna gaskiya idan suna son sake gina aminci da Iran. A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da takwaransa na Iran Mas’ud Pezeshkian, shugaban na Iran ya ce dole ne turai su mutunta ‘yancin Iran kuma su daina gabtar da […]
Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar

Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta na yin watsi da ayyata a matsayin kasa mai take hakkokin addinai da Amurka ta yi. Da yake kare tarihin Najeriya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce “barazanar Trump na ɗaukar matakin soja ba ta da tushe kuma hakan yana a matsayin […]
Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai kara karfafa zaman lafiya a yankin […]
Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba

Majalisar Tsaro ta Sudan ta ƙi amincewa da duk wani shirin tsagaita wuta, tana mai gindaya sharadin cewa sai dai idan (RSF) ta janye daga biranen da ta kwace iko da su. Majalisar ta bayyana wannan matsayin ne a wani taro da aka gudanar a babban birnin Khartoum, don mayar da martani ga shawarar tsagaita […]
Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya

Tawagar masu sa ido ta Tarayyar Afirka ta sanar a ranar Laraba cewa zaɓen Tanzania “bai cika ƙa’idodin dimokraɗiyya ba,” tana mai tsokaci kan zaɓen da aka yi jayayya a kansa wanda ya haifar da zanga-zanga mai tsanani kwanan nan. An ayyana Shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen da gagarumin rinjaye […]