Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi kira da mutane da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin raya ranar Kudus da duniya da ake yi a juma’ar karshe ta watan azumin Ramadana.
Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana hakan ne dai a yayin jawabinsa na raya dararen “lailatul-Qadari” a jiya juma’a,inda ya yi ishara da yadda wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran marigayi Imam Khumaini ( r.a) ya ayyana wannan rana.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa; A halin da ake ciki a yanzu al’ummar Gaza suna fuskantar manyan laifuka irin na dabbanci da ‘yan sahayoniya suke tafkawa a kansu, da su ka hada kisan kiyashi, yunuwa, kora daga gidaje da kuma jefa su a cikin tsoro da razana.
Bugu da kari babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma yi nuni da yadda ‘yan gwgawarmaya suke cigaba da yin tsayin daka da turjiya a gaban ‘yan mamaya tare da yin jinjina a gare su.
Insha Allah
Allah bar zumunci