A cikin sa’o’i 24 da suka gabata Falasdinawa 13 ne suka yi shahada a jerin hare-haren sojojin Isra’ila kan Gaza
Wata majiya a Asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa biyar ne suka yi shahada ciki har da yara uku, a wani harin sama da sojojin Isra’ila suka kai kan wani gida a unguwar Sabra da ke kudancin birnin Gaza.
Rahotonni sun ruwaito cewa: Harin sama da sojojin Isra’ila suka kai kan unguwar Sabra ya nufi wani gini mai hawa uku a yankin da ke cike da jama’a ba tare da wani gargadi ba, inda ya yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa biyar wadanda aka gano gawarwakinsu jim kadan bayan harin.
Shaidun ganin ido sun bayyana cewa: Ma’aikatan motar asibiti da na kare fararen hula sun fuskanci matsala wajen shiga gidan da aka kai harin saboda gobarar da ta tashi kuma sun yi aiki fiye da rabin sa’a don kashe wutar. Sun kara da cewa harin saman da sojojin mamaye suka kai ya haifar da barna mai yawa a yankin kuma ya sanya tsoro a tsakanin mazauna yankin.
Adadin Falasdinawan da suka mutu a asibitoci a Zirin Gaza a cikin awanni 24 da suka gabata ya karu zuwa 13, ciki har da mata, yara, da tsofaffi.