Iran Ta kalubalanci IAEA Kan Kin Cewa Uffan A Harin Amurka Kan Cibiyar Nukiliya ta Darkhovin

Iran ta kalubanci hukumar Kula da makamashin Nukiliya ta Dubiya IAEA, kan kin cewa uffana game da harin Amurka kan cibiyar Nukiliya ta Darkhovin a
harin Amurka akan cibiyar makamashin nukiliya

Iran ta kalubanci hukumar Kula da makamashin Nukiliya ta Dubiya IAEA, kan kin cewa uffana game da harin Amurka kan cibiyar Nukiliya ta Darkhovin a kudu maso yammacin kasar .

Iran ta yi kira ga hukumar da ta yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai wa cibiyar nukiliya da ake ginawa

Gwamnatin Tehran na sa ran Kwamitin Gwamnonin IAEA da Darakta Janar na IAEA (Rafael Grossi), za su bayyana matsayinsu a fili kan wannan batu tare da yin Allah wadai da laifin da Amurka ta aikata,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghaei a wani taron manema labarai a Tehran.

Hukumar ta (IAEA) dai ta bayyana a ranar Lahadi, cewa tana duba rahotannin harin da aka kai da daddare kan cibiyar nukiliyar ta Darkhovin da ake ginawa a Iran, Ba tare da yin Allah wadai da harin b.

Amma hukumar ta tabbatar da cewa cibiyar tana cikin matakin farko na gini kuma babu wani kayan nukiliya da ke wurin a lokacin bincikenta na karshe.

Darakta Janar na Hukumar, Rafael Grossi, ya sake nanata kiransa na dakatar da ayyukan soji kusa da duk wuraren da ke da alaka da nukiliya.

Hukumar ta kuma nuna cewa ta tuntubi Iran game da bayanan da aka fitar kuma za ta bayar da karin bayani da zarar sun samu.

Kafin hakan dai Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Iran ta fitar da sanarwar Allah wadai da wannan “harin da ta danganta da na ta’addanci kan tashar nukiliyar da ake ginawa a a kudu maso yammacin kasar.

“Harin da aka kai kan cibiyar samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin sa ido na duniya ya saba wa dokokin kasa da kasa,” in ji Hukumar a dandalin sada zumunta na X.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted