Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, sun kai harin ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka da dama a Kuwait, tare da kira ga al’ummar Kuwait da su nuna adawa da ci gaba da kasancewar sojojin Amurka a kasarsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, zuwa ga “mutanen Kuwait, IRGC ta ce kasashen Larabawa sun shafe shekaru suna karkashin ikon sojojin Amurka kuma ana amfani da su a matsayin sansanonin soji a kan Iran da sauran al’ummar Musulmi a Iraki, Afghanistan, da Falasdinu.
Sanarwar ta lura cewa kwanaki 140 da suka gabata Amurka ta kaddamar da hari kan Iran daga wadannan sansanonin, tana Allah wadai da Washington kan kashe yara ‘yan makaranta 168 a Minab da kuma kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatollah Seyed Ali Khamenei da ya yi shahada.
IRGC ta kara da cewa Kuwait “ba dole ba ne ta zama mafaka ga rundunar ‘yan ta’adda” wacce ta kai hari ga akalla kasashen Musulmi goma a cikin shekaru da suka gabata kuma ta kashe miliyoyin Musulmi, tana kira ga Kuwait da ta hana amfani da yankinta a matsayin wurin kai hare-hare kan kasashen Musulmi.
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan jiragen saman Amurka da ke filin jirgin saman Aqaba na ƙasar Jordan, ta hanyar jerin hare-haren makamai masu linzami.
A wani lamari na daban kuma, IRGC ta ce tankokin mai biyu sun fashe tare da tsayawa a Mashigar Hormuz da ke kudancin yankin a daren jiya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito.
IRGC ta ce jiragen ruwan na ƙoƙarin wucewa ta wannan muhimmiyar mashigar ruwan ƙarƙashin abin da ta bayyana a matsayin “tilastawar Amurka.”