Rundunar Sojin Saman Iran Sun Kai Hari Kan Rumbun Makaman Amurka

Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa, a wani sabon hari na jiragen sama marasa matuka ciki da kuma wani bangare na mataki na 17

Jiragen sama marasa matuka cikin na Iran sun kai wasu hare-hare kan wani wurin ajiye makamai na rundunar sojin Amurka

Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa, a wani sabon hari na jiragen sama marasa matuka ciki da kuma wani bangare na mataki na 17 na Operation Thunderbolt, ta kai hari kan wani rumbun makamai da kayan aiki mallakin rundunar sojojin Amurka ‘yar ta’adda a Kuwait.

Rundunar sojin Iran ta bayyana cewa ta kai hari kan wani rumbun makamai na sojojin Amurka ‘yar ta’adda a sansanin Al-Adiri, da kuma rumbunan kayan aiki da matsugunan sojojin Amurka a sansanin Ali Al-Salem da ke Kuwait, da wayewar gari a yau Talata, domin mayar da martani ga karya yarjejeniyoyin kasa da kasa da laifukan abokan gaba a yankunan da ba na soja ba.

Rundunar sojin ta jaddada cewa yakinta na kare ainihin asalin Iran da kuma tarihinta na shekaru aru-aru, da kuma kare mutanen da ba sa zalunci kuma basu yarda da zalunci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted