Lebanon: Adadin Shahidai Ya Karu Zuwa Fiye Da 4000

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta ce an sami karuwar yawan shahidai sanadiyyar hare-haren sojojin haramtacciyar Kasar Isra’ila zuwa 4,328.
makabartar shahidai

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta ce an sami karuwar yawan shahidai sanadiyyar hare-haren sojojin haramtacciyar Kasar Isra’ila zuwa 4,328.

Bugu da kari sanarwar ta ci gaba da cewa a wannan tsakanin wadanda su ka jikkata sun kai 12,228.

Tun a ranar 2 ga watan Maris ne dai sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka fara kai wa Lebanon hare-hare,wanda kuma ya zuwa yanzu ya tilastawa mutane fiye da miliyan daya yin  hijira bayan da ‘yan mamayar su ka rushe gidajensu da kuma korarsu daga garuruwa da kauyukansu dake kudancin kasar ta Lebanon.

Duk da cewa an cimma yarjejeniya a tsakanin Haramtacciyar Kasar Isra’ila da kuma Lebanon bisa shiga tsakanin Amurka, Haramtacciyar kasar ta Yahudawa ba ta daina kai hare-hare ba.

Gwamnatin Lebanon ta bude tattaunawa kai tsaye da Haramtacciyar Kasar Isra’ila adaidai lokacin da yankuna da dama na kudancin Lebanon din yake karkashin mamaya.

Kungiyoyin Hizbullah da Amal sun yi Allawadai da tattaunawar ta gwamnatin kasar ta bude, tare da bayyana shi a matsayin mika wuya ga abokan gaba.

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted