Kasar Rasha ta zargi kasashen Ukraine da Faransa da shiga tsare tsaren ayyukan ta’ddanci a Afrika.
Zargin na Rsaha na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro mai nasaba da kungiyoyin ta’adda a Afirka.
Moscow ta yi zargin cewa kasashen na hadin gwiwa ne a fannoni da dama da kungiyoyin ‘yan ta’addan kama daga raba bayanai da tsare-tsare zuwa samar da makamai na zamani, jiragen sama marasa matuka.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Rasha TASS, Daraktan Sashen Afirka na Yankin Sahara a Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Anatoly Bashkin, ya bayyana cewa kwararrun Faransa da Ukraine suna shiga cikin shirye-shiryen ayyukan da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke gudanarwa a nahiyar Afirka.
A cewar jami’in Rashar, an nakalto Faransa tana ba wa wadannan kungiyoyin nau’ikan bayanan sirri daban-daban, gami da bayanan tauraron dan adam.
Ya yi ikirarin cewa wannan taimakon ya taimaka wajen shirya wani hari kan Mali a ranar 25 ga Afrilu, da kuma wasu hare-hare da dama.
Mista Bashkin ya kara da cewa shigar kwararrun Faransa da Ukraine ba ta takaita ga raba bayanai ba kawai, Ya bayyana cewa suna shiga cikin shirye-shiryen aiki da kuma tura kayan yaki.
Bugu da kari, jami’in na Rasha ya bayyana cewa samfuran jiragen sama marasa matuka kirar Ukraine yanzu suna bayyana a hannun kungiyoyin ‘yan ta’adda a Afirka. Anatoly Bashkin ya ƙara da cewa an ruwaito cewa masu ba da shawara kan sojojin Ukraine suna nan a arewacin Mali—musamman a yankunan da Abzinawa ke zaune da kuma a wasu yankuna inda kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi ke aiki don horar da su dabarun aikin soja kan amfani da makamai na zamani kirar Ukraine da kasashen yamma.
A watan Satumba na 2025 kasashe membobin kungiyar kasashen Sahel (AES) sun bayyana anniyarsu ta mika batun ga Kotun Duniya kan zargin goyon bayan Ukraine da Faransa ga ta’addanci da ake shiryawa kasashensu.