Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Iran ya yi ba’a ga rashin zurfin tunani na Amurkawa
Babban mai shiga tsakani na Iran kuma kakakin Majalisar Dokokin kasar Muhammad Baqi’r Qalibaf ya yi ba’a ga bayanan sirrin jami’an Amurka, yana mai da’awar cewa Amurkawa na ci gaba da kawo sabbin kayan aikin soja zuwa yankin Gabas ta Tsakiya yayin da suke ikirarin cewa suna son dakatar da yakin.
Qalibaf ya rubuta a dandalin X cewa: “Amurkawa na ci gaba da kawo sabbin kayan aikin soja a yankin kuma suna da’awar cewa suna neman dakatar da yakin.”
Ya kara da cewa: “Sun yi zaton cewa bayanan sirrin Iran suna da iyaka kamar nasu.”
Shugaban Majalisar ya ci gaba da cewa: “Iran ta kai wani matsayi na ƙwarewa wajen gano waɗannan dabarun Amurka, kuma bisa ga wannan, ta shirya tsaf don tukarar duk wata barazana.”
Iran