Isra’ila da kasar saudiya sun tattauna bisa shiga tsakanin cibiyar tsaron Amurka ta CENTCOM don taimakawa Riyadh ta kare kanta daga hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami da dakarun sojin kasar yamen ke kai mata, ta hanyar zurfafa binciken samar da bayanan sirri
Jaridar turanci ta isra’ila Jerusalem post ta nakalto cewa wakilai daga birnin riyad da na gwamnatin isra’ila sun gana tare da tattaunawa da cibiyar dakarun sojin Amurka ta centcom ta jagoranta domin taimakawa kasar Saudiya wajen tabbar da tsaron kasarta.
Majiyar labaran ta tabbata da cewa kasar saudiya ta bukaci taimako da ake ganin zai mayar da hankali wajen bada goyon baya na samun bayanan sirri , domin samun cikakken hoto na yadda sojojin kasar yamen suka fadada karfinsu a yankin tare da gano shirye shiryen da ake yi na gudanar da ayyukan soji a nan gaba
Jaridar Bloomberg ta kasar Amurka ta bayyana cewa kasar saudiya ta roki birtaniya ta taimaka mata wajen fitar da dakarun sojin kasar yamen daga mashigar babul mandab, da kuma taimaka mata wajen kare hare haren da dakarun sojin yamen ke kai mata a muhimman wurare ayyukan manta