Yankin Kurdawan Iraki: Ba Zai Taba Bari A yi Amfani Da Yankisu Ba

yankin kurdawa na kasar Iraqi sun nuna goyon bayansu ga iran kuma ba za su bari ayi amfani da yankinsu ba

Shugaban kungiyar patriotic union of Kurdistan PUK ya bayyana cewa kasar iraki da yankin kurdawa a shiye suke su kare yankinsu kuma ba za su  taba bari ayi amfani da yankinsu wajen yin barazana ga kasashe makwabtanmu ba musamman ma kasar iran

Bafel Talabani shugaban kungiyar PUK  yayi wannan bayani ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqci a nan birnin Tehran a yau talata, yace akwai bukatar hadin guiwa mai karfi tsakanin iran da iraki wajen aiwatar da yarjejeniyoyin tsaro da aka cimma ,kuma a kwabe makaman kungiyoyin dake barazana ga tsaron kasashen guda biyu

Talibani da ke jagorantar babbar tawaga zuwa birnin  Tehran don tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin kasar iran, sun nuna goyon bayansu na ganin an fadada yin aiki tare da kasar iran a bangaren tsaro tattalin arziki da kuma cinikayya.

Ana sa bangaren ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yace kasar iran a shiye take ta kara inganta dangantarta da yankin kurdawan kasar iraki, musamman Sulaimaniya, da zai mayar da hankali wajen fadada Musayar tattalin arziki cinikayya da kuma karfafa tsaro a iyakokinsu da kuma yaki da ta’addanci

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted