Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya amince ya sayarwa Benyamin Natanyahu Firay ministan HKI boma bomai masu nauyin ton guda ko wannensu har dubu 40,000. Kima kimarsu ya kai dalar Amurka biliyon 2 da miliyon 800.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto New York time na cewa wannan cinikin shi ne mafi girma a baya bayan nan ga HKI saboda da ci gaba da kissan mata da yara a gaza da kuma mutanen yankin wadanda suka hada Lebanon da Iran da Siriya.
Labarin ya kara da cewa boma boman sun hada da MK84 mai nauyin ton guda ko wannensu har 20,000. Da samfurin BLU 117 suma 20,000 sai kuma boma boman samfurin –I guda 20,000. Da wasu 2000.
Labarin ya kara da cewa, ma’aikatar harkokin waje ta aikawa majalisar dattawa da kuma wakilan kasar don amincewa da cinikin.
Amma wasu majiyoyin HKI sun bada labarin cewa tuni ‘Congrass ta amince da wannan safakar’.
Kamfanin dillancin labaran HKI ‘Maku’ ta bada labarin cewa tuni congrass ta rika ta amince da sayarwa HKI wadannan makamai. Ya kuma kara da cewa boma bomai dubu 10 masu amfani da kwakwalwa yake gane makiya.