Najeriya: Sojojin Kasar Sun Kashe Yan Ta’adda 1,106 A Jihar Borno

Dakarun sojojin Najeriya runduna ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta bada sanarwan kashe yan ta’adda na kungiyoyi daban daban hara 1106 a cikin shekarar da

Dakarun sojojin Najeriya runduna ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta bada sanarwan kashe yan ta’adda na kungiyoyi daban daban hara 1106 a cikin shekarar da ta gabata tare da kwace kudade kimani Naira miliyon 300 daga hannunsu.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto kwamandan rundunar ta OPHK Manjo Janar Abdussalam Abubakar yana fadar haka a wani jawabin ban kwana da ya gabatar a sansaninsu dake  Maimalari na birnin Maiduguri.

Janar Abubakar yace, sun kama akalla mutane 758 wadanda suke taimakawa yan ta’addan, da makamai kimani 475 tare da albarusai 24,409 daga hannun yan ta’adda na kungiyoyin ISWAP da JAS. Haka ma sun kwace boma boma har 295 wanda kuma suka sami nasarar kwancesu ba tare da sun yi barn aba. Ya ce mayaki kimani 969 ne suka mika kansu da makamansu a cikin shekarar da ta gabata.

Janar Abubakar ya godewa sojojin da suka yi aiki da shi a matsayin babban kwamandar Rundunar, ya kuma yi masu fatan nasarori a kan sauran yan ta’adda a yankin.

Yace daga cikin wadanda aka halaka cikin shuwagabannin kungiyoyin a cikin wannan lokacin sun hada da Abu Bilal Al-Muniki (Abu Mainok), Malam Jidda (Amir of Ngorgore/ a kauyen Malumti da kuma Abu Modu, Modu Dogo. Har’ila yau da, Munzir of Dogon Chukun, Abu Aisha (Qaid of Tumbun Mota), da Abul Kaka, suna daga cikin wadanda aka halaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted