Mataimakin Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta jin tsoron yaƙi da babbar ƙasa kamar Amurka
Mataimakin shugaban Kasar Iran Muhammad Ja’afar Qaimbanah ya yi ikirarin cewa: “Iran ba ta jin tsoron faɗa da babbar ƙasa kamar Amurka ko wata ƙasa mai makaman nukiliya kamar Haramtacciyar kasar Isra’ila, Wannan ya faru ne sakamakon bayyananniyar akidar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da ya yi shahada.”
Muhammad Ja’afar Qaimbanah ya bayyana a ranar Litinin cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta jin tsoron faɗa da babbar ƙasa kamar Amurka ko wata ƙasa mai makaman nukiliya da ake kira Isra’ila. Wannan ya faru ne saboda koyarwar Marigayi Jagoran Juyin Juyi Halin Musulunci.”
Ya jaddada cewa: Maƙiyi yana da nufin lalata wayewar Iran, amma dabaru uku masu mahimmanci sun kai ga shan kayensa. Ya ce, “Babu wanda ya yi tunanin cewa: Iran za ta iya tsayawa kan manyan ƙasashen masu makaman nukiliya guda biyu a duniya. Babban dalilin nasarar al’ummar Iran shine koyarwar soja da suka samu daga Jagoran juyin juya halin Musulunci da ya yi shahada, da kuma ƙarfin kimiyya na masana kimiyyar tsaron Iran waɗanda suka sami damar samar da makamai mafi ci gaba a duniya. Ya kamata mu sumbaci hannun dukkan mayaka, injiniyoyi, da waɗanda suka zauna a bayan faifan harba makamai, suka sarrafa jiragen sama marasa matuƙa ciki, suka kuma jefar da makamai masu linzami a kan abokan gaba.”