Iran Ta yi Nasara Samun Kujera A Kwamitin Hukumar IAEA

iran tayi nasaar zama daya daga cikin mamba a babban zauren hukumar IAEA duk da makircin amurka na hana ta

Wakilin iran a majalisar dinkin duniya a birnin viyann ya bayyana cewa an zabi jamhuriyar musulunci ta iran a matsayin daya daga cikin mamba a babban zauren kwamitin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya duk da kokarin da kasar Amurka ta yi na ganin ba’a yi zaben ba.

A cikin wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na X wakilin iran a hukumar IAEA yace mambobi hukumar sun zabi kasar iran a matsayin daya daga cikin mambobin hukumar , kuma ya bayyana sakamakon a matsayin amsa ga kokari da Amurka tayi na amfani da tasirinta wajen yin matsin lamba ga hukumar na ganin ba’a zabi kasar iran ba,

Duk da kokarin Amurka wajen ganin an hana iran halartar taron babban zauren  kwamitin hukumar kula da makamin nukiliya ta duniya daga karshe dai mambobin hukumar sun dauki matakin fitar da zabinsu kuma sun zabi kasar iran.

Ana shi bangaren Behruz kamalvandi kakakin hukumar nukiliya ta kasar iran yace kasar Amurka ta dauki mummun mataki a yan kwanakin nan na ganin an hana iran halartar taron da kwamitin zai gabatar, yace dukkan mataken da ta dauka bata yi nasara ba, kuma an gudanar da zaben.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted