Iran Ta Sha Alwashin Kare Shirin Nukliyar Kasar

Iran ba zata taba dakatar da shirinta na makamashin Nukliya ba, duk tare da takurawar makiyanta. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto

Iran ba zata taba dakatar da shirinta na makamashin Nukliya ba, duk tare da takurawar makiyanta.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin jakadan Iran a hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA yana fadar haka.

Ya kuma kara da cewa duk tare da boma boman da Amurka da HKI suka yiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar da kuma kissan kwararru da masana fasahar Nukliya na kasar, ba zamu taba mika kai ga barin hakkimmu ba.

Behrouz Kamalbandi ya bayyana haka ne a lokacinda yake jawabi a taron hukumar IAEA a birnin Vienna a ranar Talata. Ya kuma kara da cewa makiya tare da taimakon hukumar IAEA ba zasu iya tumbuke fasahar Nukliyar daga cikin kasar Iran ba saboda karatun ya yi jijiyoyi a kasar.

Ko da zasu sami nasarar shafe duk abinda muka mallaka na shirin makamashin Nukliya muna da masana kwararru wadanda zasu sake gina su tun farko.

Kamalvandi ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran ta yanke shawarar tafiyar da shirinta na makamashin Nukliya ne bayan da ta gamu da yaudara daga wasu kasashen duniya wadanda basa son iran ta mallaki wannan fasahar. Yanzun kuma sun yi lettin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted