Malamai Sun Yi Tir Da Kisan Da Wasu ‘Yan Ta’adda Suka Yi Wa Wani Malamin Sunna A Iran

shuwagabannin kabilu dana addini sun yi tir da kisan gillar da akayi wa babban malamin ahlu sunna a iran

Rahotanni sun bayyana cewa shuwagabanin kabilu  da malaman addini da manyan masu fada aji da sauran alummar yankin sistan Baluchistan sun yi tir da kisan gillan da aka yi wa molavi Yousef Gorji fitattacen malamin ahlu sunnah a kasar iran

A cikin wani bayani da suka fitar a yau talata dukkan bangarorin da suka sanyawa hannu a takardar sun bukaci a gudanar da bincike don gano wadan suka aikata  kisan gillan da kuma gurfanar da su gaban shari’a domin su fuskanci hukuncin danyen aikin da suka aikata

Haka zalika bayanin ya jaddada cewa akwai bukatar wayar da kan jama’a da kuma sadaukarwa, kuma ya yi gargadin cewa wadanda suka gudanar da kisan gillan sun yi shi ne don kulla makirci na haifar da rashin zaman lafiya da tsaro  da kuma tarzoma musamman a yankin kudu maso gabashin kasar

Daga karshe sun ce babban burin makiya shi ne haifar da rashin tsaro shi yasa suka kashe fitaccen mutum kuma mai tasiri kuma mai kima, domin haifar da rarrabuwar tsakanin mutane don tarwatsa zaman lafiya a yankin baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted