IRGC: Katapaten Jirgin Mai Ya Gamu Da Nakiya A Hurmuz

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran IRGC reshen ruwa wto Navy sun bada labarin gamuwar wani kataparen jirgin dakon mai a mashigar

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran IRGC reshen ruwa wto Navy sun bada labarin gamuwar wani kataparen jirgin dakon mai a mashigar ruwa ta Hurmuz bayan ya gamu da nakiya ta tashi ta kuma lalatata ta kuma tada gobara a cikinsa.

Kamfanin dillancin labaran -Pars Today- ya nakalto majiyar na cewa, jirgin mai suna Al-Ghayah ya gamu da nakiyar ce a dai dai lokacinda yake bin haramtacciyar hanya ta wucewa daga mashigar. Har’ila yau jirgin yana dauke da lamba 9325336 na jiragen ruwa.

Labarin ya kara da cewa hakan ya faru ne a jiya Talata, kuma wani kokarine na kasar Amurka ta sake bude wannan mashigar musamman a dai dai lokacinda yake yakin neman zabe a kasar, kuma inda ya sha kariyawa masu sauraronsa kan cewa ai ya rika ya bude mashigar ruwa ta Hurmuz.

Majiyar ta IRGC ta kara tabbatar da cewa mashigar zata ci gaba rufewa har zuwa lokacinda Amurka zata cika sharuddan da Iran ta shimfida na bude mashigar.

Banda wannan wasu labaran ta IRGC sun tabbatar kakkabo jirgin Drone na makiya a mashigar ruwa ta Hurmuz a jiyan, smafuri MQ-1 kuma wannan shi ne na 5 tun bayan safe komawa yaki na baya bayan nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted