Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa samun mtanen kasar Iran a kan tiyunan kasar tun dare na farkon da HKI da Amurka suka farwa kasar da yaki ya nuna cewa fatan makiya ne ta zama zane kan ruwa, amma mutane ne suka sami nasara a kansu na tsawon darare 200 a yau.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar kuma shugaban tawagar tattaunawa ta kasar Iran ya bayyana haka ne a wai jawabin da ya gabatarwa mutanen kasar saboda ciki darere 200 da jajircewarsu a kan titunan birane da garuruwan kasar na tsawon wannan lokaci.
Yace kowa daga cikin jami’an gwamnati da Sojoji da sauran Jami’an tsaro suna aikinsu kamar yanda ya dace, amma goyon bayan mutane tare da fitowa kan tituna, babu sanyi babu zafi don kare kasarsu yana da matukar muhimman a wannan yakin da ake fafatwa da mafi munin kasashea duniya..
Fitowar mutane a kan tituna yana bawa sojojin kuzarin yin aikinsu ba tare da fargaban cewa makiya suna iya kutsawa cikin gari su kwace kasar a yayinsu su kuma suna aiwatar da aikinsu ba. Qalibaf fitowar mutane a kan tituna a kuma cikin dare, ya nuna cewa akidun juyin juya halinmuslunci a kasar Iran sun kafu a cikin zukatan mutanen kasar Iran. Babu kuma wanda ya isa ya fitar da shi cikin zukatansu, ko da kuwa sun yi amfani da mafi munin makamai a kansu.
Tun daren 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar Ne jiragen yakin HKI da kuma na Amurka suka farwa kasar Iran da yaki suka kuma fara da kashe Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyed Aliyul Khaminaei, mutane suka kan titun a cikin dararen kwanakin yakin, wanda a yau yake cikin darare 200.