Saudia Ta Nemi Taimakon HKI Kan Yaki Da Huthawa

Kafafen yada labarai na HKI sun bada labarin cewa yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudia Muhammad bin Salman ya bukaci taimakon HKI a yakin

Kafafen yada labarai na HKI sun bada labarin cewa yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudia Muhammad bin Salman ya bukaci taimakon HKI a yakin da take fafatawa da Huthawa na kasar Yemen.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Jaridar Hayom ta HKI tana fadar haka ta kuma kara  da cewa, da farko bin Salman ya nemi taimakon kasashen larabawa na yankin tekun farisa sannan a fakaice ya bukaci taimakon bayanan asiri na soje daga HKI don samun nasara a kan kungiyar ta Ansarallah.

A fafatawa da dakarun kungiyar a cikin yan makonnin da suka gabata dai, sojojin haya na kasar Saudia sun sha mummuna kaye a hannun Ansarallah, wadanda suka kwace yankin masu yawa daga hannun sojojin hayan saudia, har zuwa tsibiran Mocha, Zuqar da kuma Perim  da ke kan mashigar ruwa ta babul mandab wanda ya hada tekun maliya da Tekun Aden.

Hayom tace saudia ta gabatar da bukatar ta hannun rundunar CENTCOM ta kasar Amurka a yankin. Kafin haka shugaban Trump ya ki tankawa MBS a kan wannan bukatar.

Sannan Turkiyya da Pakistan wadanda suka sanya hannu kan yarjeniyar tsaro da Saudia kimani wata guda da ya gabata suna taka tsantsan da shiga rikicin. Sai kasar  mAsar wacce ta tausawa saudia saboda idan an rufe babulmandab hakan zai shafi mashigar ruwa da Swiz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted