Araqchi: Iran Ta Yi Nasara Kan Runduna Mafi Girma A Duniya

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran  sun yi nasara a kan rundunar soja mafi girma a duniya Ministan Harkokin Wajen kasar Iran

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran  sun yi nasara a kan rundunar soja mafi girma a duniya

Ministan Harkokin Wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya jaddada cewa: Dakarun sojin Iran sun sadaukar da rayukansu a yakin da aka yi kwanan nan tare da samun nasara kan abin da ya bayyana a matsayin rundunar soji mafi girma a duniya. Wannan ba kawai kalamai ne na siyasa ba, a’a, gaskiya ce da duniya baki daya ta shaida.

Ministan ya bayyana cewa, a yayin yakin, Jamhuriyar Musulunci ta nuna wa duniya cewa ita babbar kasa ce mai karfi da ba a iya cin nasara a kanta. Ya kara da cewa: “Ya sha jin ministoci da jami’an wasu kasashe suna cewa: ‘Ku ‘yan Iran kun yi abin al’ajabi; kun ba duniya baki daya mamaki.'”

Ya ci gaba da cewa babu wanda ya yi tsammanin Iran za ta iya tsayawa tsayin daka ta wannan hanya a gaban Amurka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya—wadanda dukkan kasashen Yamma da wasu kasashen da aka sani suke goyon baya—har ta kai ga tilasta wa makiyin neman tattaunawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted