Larijani: Iran Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Tare Da Lebanon A Kowane Hali

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta kasance tare da al’ummar Lebanon a koyaushe Sakataren majalisar koli ta tsaron

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta kasance tare da al’ummar Lebanon a koyaushe

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya tabbatar da cewa: Alakar al’adu tsakanin Iran da Lebanon ta taimaka wajen karfafa alaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Beirut a yau Laraba, Larijani ya yi nuni da cewa, Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Lebanon.

Larijani ya kara da cewa: Iran da Labanon suna da dadaddiyar wayewa, kuma a ko da yaushe akwai alaka ta kut-da-kut a tsakanin al’ummomin kasashen biyu. Ya kara da cewa, wannan alaka ta al’adu ta haifar da alaka ta musamman tsakanin al’ummomin kasashen biyu, ta yadda a lokacin da al’ummar kasar Labanon ke cikin wahala, al’ummar Iran su ma suna jin wannan zafi.

Haka nan kuma ya bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tsayawa tsayin daka a kan al’ummar kasar Lebanon a kowane hali, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu wajen fuskantar kalubalen da suke fuskanta.

Da yake karkare jawabinsa, Larijani ya bayyana muhimmancin tarukan da zai yi a yau Laraba tare da shugaban kasar, da shugaban majalisar dokoki, da fira minista, da kuma wasu ‘yan siyasar kasar ta Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted