Search
Close this search box.

Sabon Jakadan Nijar A Iran Ya Mika Kwafin Wasikun Fara Aiki

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na riko, Ali Bagheri Kani ya karbi kwafin wasikun fara aiki na sabon jakadan Jamhuriyar Nijar a kasar.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na riko, Ali Bagheri Kani ya karbi kwafin wasikun fara aiki na sabon jakadan Jamhuriyar Nijar a kasar.

Yau Litinin 12 ga watan Agustan 2024, Malam Seydou Zataou Aly, ya mika wasikun nasa a matsayin sabon Jakadan Jamhuriyar Nijar a Iran.

Yayin ganawar bangarorin biyu sun jaddada aniyar kasashensu na ci gaba da karfafa huldar hadin gwiwa a fannoni daban daban.

Sun tattauna batutuwa daban-daban na hadin gwiwarsu tare da maraba da ingancin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A tare sun yi alkawarin yin aiki don karfafawa da daidaita dangantakarsu, musamman yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai a ziyarar da firaministan Nijar, Mohamed Lamine Zein ya kai a watan Janairun 2024 a Tehran, inda aka rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a fannonin makamashi, kiwon lafiya masana’antu da al’adu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments