Sojojin Sudan sun sanar da samun nasara kan ‘yan tawayen kasar na rundunar Rapid Support Forces a yakin garin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa
Tashar talabijin ta Aljazeera ta watsa rahoton cewa: An yi arangama tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, a garin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa, garin da aka kwashe makonni ana gwabza fada a cikinsa, wanda hakan ya haifar da damuwa ga kasashen duniya.
Rundunar sojin Sudan ta ce: Dakarun hadin gwiwar kungiyoyin masu dauke da makamai da sojojin kasar sun fatattaki abin da ta kira ‘yan ta’adda, dangane da kungiyar Rapid Support Forces, a wani gumurzu da aka yi a tsakaninsu a birnin El Fasher. Kuma rundunar sojin ta jaddada cewa: Sojojinta sun yi nasarar tarwatsa wasu motocin yakin ‘yan tawayen tare da kwace wasu.