Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da kwace jiragen ruwa biyu masu dauke da mai da suka karya yarjejeniya a mashigar tekun Hormuz
Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC) ta sanar da cewa: An kai hari kan jiragen ruwa guda biyu na mai kuma an kama su da sanyin safiyar jiya Juma’a bayan sun bi ta wata hanya mara aminci kuma haramtacciyar hanya.
Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci “IRGC” ya fitar da Sanarwa Mai Lamba 57 game da Operation Nasr 2, wanda ke cewa: “Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC, suna ci gaba da iko da cikakken bada tsaro a kan Mashigar Hormuz da kuma kare amanar da al’ummar Iran masu aminci suka dora musu.”
Ofishin Hulɗa da Jama’a na IRGC ya ci gaba da cewa: “Da sanyin safiyar ranar Juma’a, an kai hari kan jiragen ruwa guda biyu na mai bayan sun bi wata barauniyar hanya mara aminci kuma haramtacciyar hanya, sakamakon yaudarar CENTCOM. Sun yi kuskuren zaton za su iya ketare Mashigar Hormuz ta hanyar da ba ta da halacci, ƙarƙashin umurnin sojojin Amurka, ba tare da yin la’akari da gargadin IRGC ba. Wasu jiragen ruwa guda huɗu na mai sun canza hanya cikin sauri suka koma inda suke.”
Ofishin Hulda da Jama’a na IRGC ya kara da cewa: “Rundunar Sojan Ruwa ta IRGC ta sake gargadin cewa tsoma bakin da sojojin Amurka ke yi kan bada umarnin da ba bisa ka’ida ba ga jiragen ruwa a yankin ba zai zama abin da za a amsa ba.”