Falasdinawa  2 Ne Suka yi Shahada Sakamakon Hari Sojojin Israila A Gaza

Jiragen sama marasa matuki na isra’ila sun kai hari a yankin Gaza kuma sun yi sanadiyar shahadar falasdinawa guda biyu a ci gaba da keta

Jiragen sama marasa matuki na isra’ila sun kai hari a yankin Gaza kuma sun yi sanadiyar shahadar falasdinawa guda biyu a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suke yi , da kuma tattaunawar da ake yi tsakanin tel aviv da kuma kungiyar gwagwarmaya ta hamas yanzu  

Majiyoyin labarai sun bayyana a yau Asabar cewa falasdinawa guda 2 sun yi shahada wasu da dama kuma sun jikkata  a hare-hare daban daban da isra’ila ta kai da jiragen sama marasa matuki a titin salah al-din, da al-mahatta da kuma Deir al-balah a tsakiya  yankin gaza.

Haka zalika isra’ila ta kai hari kan masallacin Khadija dake birnin Gaza , haka kuma ta kai hari a sansanin yan gudun hijara na darul balah dake yankin al-saftawi dake gaza, shi ma masallacin al-shuhada dake sansanin yan gudun hijira na Nusairat akalla mutane 10 ne suka jikkata,

Hare-haren da Isra’ila ta kai a yankunan daban- daban a zirin gaza da goyon bayan Amurka tun a ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023  sun kashe falasdinawa 73341 tare da jikkata 174086 kuma sun rusa kashi 90 cikin dari na muhimman gine gine dake gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted