Iran Tace Babu Wanda Zai Wuce Ta Shigar Hurmuz Sai Da Izinin Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran

Ofishin hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci na kasar iran ya sanar cewa mashigar hurmzu a rufe take ruf,  kuma babu wani  shige

Ofishin hulda da jama’a na dakarun kare juyin musulunci na kasar iran ya sanar cewa mashigar hurmzu a rufe take ruf,  kuma babu wani  shige da fice da zai gudana ta wajen ba tare da hadin guiwa da dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran ba,

Wannan sanarwar ta fito ne bayan da hedkwatar Centcom ta Amurka ta tafka karya, dake cewa batun shige da fice ta mashigar Hurmuz yana gudana kamar yadda aka saba kuma dukkan kamfanin sufurin jiragen ruwa suna iya wuce ba tare da wata matsala ba karkashin kulawar Amurka, lamarin da iran ta karyata kuma ta yi watsi da shi baki daya.

A jiya jumaa dakarun kare juyin musulunci ta iran sun fitar da wata sanarwa  mai lamba 57 cewa dakarunsu sun kai hari kan wasu tankokin dakon mai guda biyu da suka nuna taurin kai a mashigar Hurmuz  yayin da wasu tankokin mai guda 4 suka yi gaggawar komawa zuwa sansaninsu a nan take .

a cikin wani bani da tayi na mayar da martani kan bayanan karya da hedkwatar centcom ta watsa, yace “mun sanar da dukkan kamfanonin sufurin jiragen ruwa da kada su mayar da hankali kan bayanan da Centcom ta fitar, su tambayi wadanda suka fada cikin tarko saboda yarda da bayanan karya da ta sanar , yanzu suna cikin tsaka mai wuya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted