Hizbullah Ta yi Kira Ga Gwamnatin Labanon Da Ta yi Aiki Da Nauyinta Na Kawo Karshen Ta’addancin Isra’ila

Rahotanni da suka fito dga kasar Labanon sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulla ta ja hankalin gwamnatin labanon  kan muggan ayyukan da isra’ila take

Rahotanni da suka fito dga kasar Labanon sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulla ta ja hankalin gwamnatin labanon  kan muggan ayyukan da isra’ila take tafkawa a kudancin kasar, kuma tayi kira gareta da ta da tayi aiki da nauyin da ke kanta na dakatar da isra’ila game da ci gaba da rushe- rushe da yyuakan ta’addanci da takeyi  a kauyukan dake kudancin labanon

A cikin wani jawabi  da kungiyar ta fitar a jiya jumaa hizbullah ta yi nuni game da yadda isara’ila take ci gaba da aikata muggan laifuka a kudancin labanon, inda take rusa kauyuka da kona gidaje da kuma markade hanyoyi da filaye , da kuma rusa makarantu da Asibitoci da kashe fararen hula a farmaki da take kai musu don hana su komawa gidajensu da kauyukansu don ci gaba da rayuwa.

Kungiyar hizbulla ta zargi yin gum da baki da gwamnatin berut ke yi  kan ta’addanci da isra’ila, a matsayin wata alama ta amincewarta da ya bada dama Isra’ila ta ci gaba da mamaye yankunan labano da kuma cin karensu ba babbaka

Yarjejeniyar da aka cimma a ranar 26 ga watan yuni ta bukaci Isra’ila ta janye daga dukkan yankunan da ta mamaye a kudancin labanon daidai lokacin da ake baza sojojin labanon a yankunan da suka fice. amma tun daga wannan lokacin zuwa yanzu Isra’ila na cigaba da kai hari a kudancin labanon da kuma rushe- rushe a kan iyakarta da labanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted