Iran Ta Gargadi Birtaniya Cewa Za Tayi Amfani Da Karfinta Wajen Kare Kanta

Ministan harkokin wajen kasar iran Abass Araqchi ya gargadi gwamnatin Birtaniya game da duk wani yunkuri na taimakawa wajen kai mata hari , kuma yayi

Ministan harkokin wajen kasar iran Abass Araqchi ya gargadi gwamnatin Birtaniya game da duk wani yunkuri na taimakawa wajen kai mata hari , kuma yayi wannan gargadin ne a wata tattunawa da yayi ta wayar tarho da takwaransa na kasar Birtaniya  Ed Miliband  a jiya jumaa.

Haka zalika yayi ishara cewa karkashin dokokin kasa da kasa da kuma ma’anar kudurin kai hare-hare, idan aka bari mahara suka yi amfani da yankin wata kasa don kai hari kan wata kasa ta daban ba bisa ka’ida ba to ya zama hari na ta’addanci, kuma wannan kasar tana da hakkin kare kanta wajen kai hari a inda aka kawo mata

A ranar 21 ga watan yuli da ya gabata fira ministan birtaniya Any burnham ya amince Amurka ta yi amfani da sansaninta wajen kai wa kasar Iran hari, ya ci gaba da amfani da siyasar da aka kirkirota tun lokacin tsohon fira ministan da ya sauka keir Stermer.

Daga karshe Araqchi yayi tir da mataken rashin Adalaci da birtaniya take dauka kan kasar ,kuma yace iran za ta mayar da martani  kan duk wani hari da Amurka za ta kai mata da kuma duk wata kasa da ta hada kai da Amurka wajen kai  mata hari

Ana sa bangaren sakataren harkokin wajen birtaniya  Miliband yace kasar sa ba ta cikin bangaren dake yaki da iran, kuma ta yi Imani da diflomasiya wajen waraware matsalolin da ake da su, ya kara da cewa akwai bukatar yin riko da hanyar diflomasiya domin kara bunkasa dangantakar dake tsakani da kuma rage yawan fituntunin dake tasowa a yankin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted