Aragchi: Aikin Kafafen Yada Labarai Ne Yada Gaskiyar Abinda Ke Faruwa A Kallafeffen Yaki Na Uku

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aikin kafafen yada labarai ne su yada abubuwan da ke faruwa a yakin da Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aikin kafafen yada labarai ne su yada abubuwan da ke faruwa a yakin da Amurka ta dorawa JMI na kwanaki 40 da kuma wanda ake ciki a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau Asabar a taron kafafen yada labarai wanda aka gudanar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran dake nan birnin Tehran.

Ministan ya kara da cewa, a ayyukan diblomasiyya da suke yi a ma’aikatar,kafafaen yada labarai ne, suke taimakawa su yada shi a duniya don isa ga dukkan wadanda suke neman gaskiya.  Yace makiya suna amfani da kafafen yada labaransu don farfagandar  karaya dangane da yakin, don haka kafafen yada labarai. Yace nasarar ayyukan diblomasiyya ya dogara da ayyukan kafafen yada labarai na ko wace kasa ce a duniya.

Taron na kafafen yada labarai ya sami halattan shugaban kamfanin dillancin labaran IRNA na gwamnatin kasar Iran, Hossain Jaberi, Ilyas Hazrati shugaban ma’aikatar yada labarai na gwamnatin kasa, mataimakin ministan harkokin waje kan al-amuran sharia da kuma kasa da kasa Kazem Gharib Abadi, wanda kumaya wakilci ministan harkokin wajne kasar. Sai kuma kakakin gwamnatin Iran Fatimah Muhajirani, da esmail Baghaeei kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar da sauran manya manyan shuwagabannin kafafen yada labarai a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted