Manya manyan jami’an sojojin Iran sun bayyana cewa, suna da wani shiri na musamman na maida martani ga Amurka idan ta kuskura ta aiwatar da baraznar da takewa kasar.
Kamfanin dillancin labaran tasnim ya nakalto jami’an sojojin suna cewa ‘suna sani da shiri ko kuma barazanar Amurka na kaiwa manya manyan ayyuka kamar hanyoyi da gadoji da kayakin wutan lantarki da sauransu, na kasar Iran a cikin yan kwanaki masu zuwa, ‘ sun kara da cewa a maida martani zasu lalata irin wadan nan kayaki na Amurka da HKI a yankin, wadanda suka hada da kamfanoninsu a yankin da kuma a cikin HKI’.
Jami’an sojojin sun kara da cewa sojojin Iran a cikin yakin kwanaki 40 da kuma na makonnin da suka gabata sun tabbatarwa duniya kan cewa suna da karfin aiwatar da hakan.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sha alwashin lalata manya manyan ayyukan jama’a a kasar Iran wadanda zasu gurgurta layuwa a kasar, a cikin yan kwanaki masu zuwa. Shugaban ya ce yana shirin farwa kasar Iran da yaki, inda zai farfasa dukkan manya manyan ayyuka a kasar Iran wanda zaimaida su baya, daga cikin har da manya manyan hanyoyi da gadoji da cibiyoyin bada wutan lantaki da madatsun ruwa da sauransu. Wadanda zasu gurgunta rayuwar mutanen kasar. Kuma yace zai yi haka ne don tilastawa gwamnatin kasar amincea da duk abinda yake so ta yi. Wadannan mummunan hare hare dai, idan ta aiwatar da su yana da ga cikin laifukan yaki. Du da cewa tana iya aikata hakan kamar yadda ta kashe yanmakaran da malamansu kimani 160 a garin Minab amma suma zasu gamu da maida martani irinsa ko fiye da shi a yankin.